UNICEF Ta koka kan Halin Da Yara Ke Ciki a Arewa maso Gabas
UNICEF Ta Bukaci A Mayar da Hankali Kan Ilimi, Abinci Mai Gina Jiki da Rigakafi Ga Yara a Arewa maso Gabas

Maiduguri, Borno, Babban jami’ar UNICEF a Najeriya, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatif, ta bayyana cewa akwai buƙatar a mayar da hankali sosai wajen inganta lafiyar yara ta hanyar samar da abinci mai gina jiki, tabbatar da samun ilimi, da kuma rigakafi, musamman a yankin Arewa maso Gabas da ya fi fama da tasirin rikici da fatara.
Wafaa ta yi wannan bayani ne yayin ziyarar ta kai ofishin UNICEF a Maiduguri, inda ta yaba wa gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, bisa shugabanci nagari da kwarewa da yake nunawa wajen kula da al’ummar jihar.
Ta ce:
Muna matukar yaba wa gwamnan jihar Borno bisa yadda yake gudanar da shugabanci da kwarewa, kuma muna tabbatar da ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar wajen inganta rayuwar kananan yara da iyayensu a wannan yanki da sauran Arewa maso Gabas.
Babbar jami’ar ta bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara, UNICEF tare da abokan hulɗarsa sun gudanar da ayyuka da dama a Arewa maso Gabas. Wadannan ayyuka sun haɗa da:
Shirye-shiryen ilimantarwa domin rage yawan yara da ke waje da makaranta.
Shirye-shiryen ciyar da yara da nufin magance malnutrition (rashin abinci mai gina jiki) da ya addabi dubban yara a yankin.
Shirye-shiryen taimakawa iyaye, musamman mata masu juna biyu da masu shayarwa, wajen samun kula ta lafiya da horo kan yadda za su kula da lafiyar ’ya’yansu.
Wafaa ta jaddada cewa babban ƙalubale a yanzu shi ne karuwar yara da basa zuwa makaranta a Arewa maso Gabas. Ta bayyana cewa UNICEF na ganin ilimi a matsayin babban ginshiƙi na farfado da yankin daga tasirin rikici.
Samun abinci mai gina jiki da ilimi ga yara ba kawai zai inganta lafiyarsu ba ne, har ma zai rage yawan yara masu fama da rashin lafiya da kuma ƙaruwa cikin wadanda ba sa zuwa makaranta, in ji ta.
UNICEF ta jaddada aniyarta na ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin Najeriya da sauran abokan hulɗa, musamman a yankin Arewa maso Gabas, domin tabbatar da cewa yara sun samu ilimi, lafiya, da kuma abinci mai gina jiki.
Wafaa ta ƙara da cewa UNICEF ba wai kawai tana mai da hankali kan yara ba, har ma tana tallafawa iyaye, musamman mata, wajen samun damar kula da iyalansu da tsayawa da kafafunsu ta hanyar ilimi da horo.
Ta kuma yaba da irin kokarin gwamnatin jihar Borno a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum wajen bada fifiko ga harkar ilimi da kiwon lafiya, tare da tabbatar da cewa an samu tsaro da ci gaba a matakai daban daban.