Yan Sanda Sun Ceto Tsohuwa Yan Shekara 80 a Jigawa, Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Kama Wasu 5

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta samu nasarar ceto wata tsohuwa ‘yar shekaru 80 da aka sace daga Minjibir a Jihar Kano, tare da kashe wasu mutum biyar daga cikin masu garkuwa da mutane da kuma kama wasu biyar a wani samame na hadin gwiwa a karamar hukumar Garki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP A. T. Abdullahi, ya ce an gudanar da wannan aikin ceto ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri da kuma nazarin fasaha, wanda ya kai su ga cafke da kashe masu laifin.
Rahoton ya bayyana cewa a ranar 16 ga Mayu da misalin karfe 1:30 na dare, bayan samun rahoton cewa wasu ‘yan bindiga kusan 12 dauke da babura guda biyar sun sace Hajiya Hajara daga Minjibir, rundunar ta hada kai da ofisoshin Gagarawa, Gumel, Garki da Sule-Tankarkar, tare da goyon bayan masu gadi Fulani da mafarauta na daji karkashin jagorancin ACP Bala Umar, Kwamandan na Gumel, inda suka kai farmaki ga maboyar masu laifin.
Maboyar sun hada da Wadi Fulani Settlement, GGW Tagwayen Fage, Wusada Fulani Settlement da Katoro Fulani Camp, duk a Garki LGA.
A yayin farmakin, musayar wuta ta barke tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindigar, wanda hakan ya kai ga hallaka mutum biyar daga cikinsu, tare da cafke wasu biyar da harbin bindiga a kafafunsu, ciki har da shugaban kungiyar, Yahaya mai shekara 35 daga Katoro Fulani Camp.
An ceto Hajiya Hajara ba tare da rauni ba, kuma an kwato bindigogi biyu kirar AK-47, bindiga kirar LAR tare da harsasai 14, babura guda biyu da wayoyi guda biyu.
Dukkan wadanda aka kama da wadanda aka kashe an kai su asibitin Gumel General Hospital don kulawa da kuma tantancewa.
Wata majiya daga rundunar ta tabbatar da cewa ba a biya kudin fansa ba, kuma babu jami’in tsaro da ya ji rauni a lokacin aikin ceto.