Labarai

‘Yan sanda sun kori jami’i kan kisan matashi a Delta

Rundunar yan sanda bayyana korar wani jami’inta, ASP Nuhu Usman, bayan samun sa da hannu a kisan wani matashi a yankin Effurun da ke jihar Delta a Kudu maso Kudancin Najeriya.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar ranar Laraba, ta ce an kammala bincike kan lamarin kamar yadda Olatunji Disu ya bayar da umarni, inda aka gano jami’in da laifi.

Kakakin rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya ce an kama matashin mai shekaru 28, Mene Ogidi, ne yayin da ake zargin yana kokarin isar da wani abu da ake kyautata zaton bindiga ce da harsashi hudu, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.

Bayan samun rahoton, aka mika binciken zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja domin zurfafa bincike.

Sanarwar ta ce binciken ya nuna cewa jami’in ya aikata laifin da ya saba wa dokokin aikin ‘yan sanda, musamman dokar amfani da makami ba bisa ka’ida ba da kuma rashin ladabi.

Rundunar ta bayyana cewa abin da ya faru ya saba wa rantsuwar aiki da jami’in ya yi na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ta kuma ce bayan kammala dukkan matakan ladabtarwa, za a mika wadanda abin ya shafa ga hukumomin shari’a domin daukar matakin doka

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker