Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed Ya Yi Jimamin Rashin Sani Abdulhamid Galaje (Galajen Kaura)

A yau, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana babban jimami da rashi na wani fitaccen masoyin sa da kuma ginshikin al’umma, Sani Abdulhamid Galaje (Galajen Kaura), wanda ya rasu bayan fama da jinya.
Gwamnan ya wallafa sakon alhini tare da jajantawa iyalai, abokan arziki, da duk wanda rashi na Galaje ya shafa. A cikin kalamansa, Gwamnan ya ce: Mutuwa rigar kowa ce. Rabuwa mafi zafi ita ce wacce aka yi ba tare da sallama ba. Rashin masoyi na hakika wanda ke ƙaunar ka ba don abin hannunka ba, matsayi ko mukami, shi ne mafi raɗaɗi. ya bayyana hakan ne a yayin da yake jimamin rashin Sani Abdulhamid Galaje, wanda aka fi sani da “Galajen Kaura”.
Marigayin ya rasu bayan fama da jinya, abin da ya bar babban giɓi a zukatan iyalai, abokai, da duk wanda ya san shi. Gwamna Bala ya bayyana Galaje a matsayin mutum mai halin kirki, wanda zumuncinsa da kyautatawa ya kasance abin misali ga al’umma.
Gwamnan ya ce wannan rashi babban darasi ne da ke tunatar da mu cewa rayuwa ba ta da tabbas, kuma ya dace mu kasance masu kyautatawa da taimakon juna. Ya kuma yi addu’ar cewa Allah ya sa jinyar da marigayin ya sha ta zama silar kankare dukkan zunubansa, ya gafarta masa, ya kuma sanya shi cikin rahamarSa.
Yana mai jajantawa iyalai da masoyan marigayin, Gwamna Bala ya ce wannan rashi babban raɗaɗi ne ga Jihar Bauchi da al’ummar da marigayin ya yi wa hidima ta hanyar ayyukansa na alheri. Allah ya kyautata makwancinsa, ya jikanmu duka lokacin da ajali ya riske mu. Allah ya ba wa iyalansa da duk wanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban giɓi.