Bauchi: Gwamna Bala ya kaddamar da rabon kayan tallafi
Gwamna Bala Muhammad ya kaddamar da rabon kayan tallafin abinci da masarufi na yaKi da yaduwar cutar corona a jihar Bauchi.
Yayin bikin kaddamarwan da ya gudana a BSADP, Gwamna Bala Muhammad yace rabon na cikin shirin gwamnatinsa samar da tallafin da saukaka rayuwar al’umar jiha musamman a wannan lokaci da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki.
Gwamnan sai ya yabawa kwamitin samar da raba tallafin kan ayyukan su na tattara kayyayakin da kuma gudummawar kudade.
Gwamna Bala sai ya gargadi kan karkatar da kayan inda yace gwamnatinsa ba za ta lazumci guluwi ba.
Rabon kayan ya gudana kamar haka;
Alkaleri 6,500
Bauchi 8,000
Bogoro 3,500
Dass 3,500
Dambam 4,000
Darazo 5,000
Gamawa 5,000
Ganjuwa 5,000
Itas Gadau 4,000
Jamaare 3,500
Katagum 7,000
Kirfi 4,000
Misau 5,000
Ningi 6,000
Shira 5,000
Tafawa Balewa 5,000
Toro 6,500
Toro 6,500
Warji 3,500
Zaki 4,000
A nasa tsokacin, mataimakin gwamna kuma shugaban kwamitin yaKi da yaduwar cutar corona da zazzabin Lassa a jiha Sanata Baba Tela yabawa gwamna Bala Muhammad yayi kan tallafi da goyon bayan da yake bada kwamitin kan ayyukan su.
Shima da yake jawabi shugaban kwamitin samar da raba tallafin me martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu yayi alkawarin samar da adalci yayin rabon.
Jami’an gwamnati ciki har mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jiha Hon Danlami Kawule, Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Mohammed Sabiu Baba, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Dakta Ladan Salihu, kwamishinoni da manyan baki.