Yadda Iran ta kauce shingen Amurka ta hanyar “shadow fleet”

Rahotanni sun bayyana yadda Iran ta yi amfani da wata cibiyar jiragen ruwa da ake kira “shadow fleet” domin kauce wa shingen ruwa da United States ta kakaba a yankin Strait of Hormuz.
Wannan hanyar ta hada da amfani da tutoci na bogi, kamfanonin karya, da kuma kashe na’urorin gano inda jiragen suke domin boye motsin su a teku.
Rahotanni sun nuna cewa duk da tashin hankali da ya biyo bayan rikicin soja tsakanin Iran da Isra’ila da Amurka, wasu jiragen ruwa na kasuwanci sun ci gaba da ketare mashigin cikin kwanciyar hankali ta hanyar wannan tsarin boye hannun.
Lamarin ya biyo bayan rahotannin harin da aka kai wa jirgin dakon kaya na Thai, Mayuree Naree, a ranar 11 ga Maris yayin da yake wucewa mashigin Hormuz, inda aka lalata injin jirgin kuma wasu ma’aikata suka rasa rayukansu.
Bayan haka, Iran ta yi barazanar rufe ko takaita zirga-zirgar jiragen abokan gaba a mashigin, wanda ke da matukar muhimmanci wajen safarar kusan kashi daya cikin biyar na man fetur na duniya.
Bayan wani wucin gadi na tsagaita wuta a watan Afrilu, Amurka ta kakaba shingen ruwa kan tashoshin Iran, amma duk da haka, bayanan bin diddigin jiragen ruwa sun nuna cewa zirga-zirga ba ta tsaya gaba daya ba kamar yadda ake zato.
Masana harkokin ruwa sun ce wannan “shadow fleet” na aiki ne a wajen dokokin kasuwancin teku na duniya, wanda ke sa gano motsin jiragen ya zama da wahala sosai.





