Labaran DareLabaran Murya

Labaran Dare Na Yau Alhamis 25 Yuni 2026 Hausa360

Saurari cikakken Labaran Dare Na Yau Alhamis 25 June 2026 Hausa360

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani kwamiti na musamman domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su a jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya fitar da sanarwar. Ayyukan kwamitin sun hada da gano manyan wuraren hada-hadar miyagun ƙwayoyi, kai samame, da tattara bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. Gwamnan ya bukaci al’umma su kai rahoton duk wani aiki da ke da alaka da miyagun ƙwayoyi.

Rukunin ƴan Najeriya na biyu sun dawo gida daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan jinkiri sakamakon tashe-tashen hankula masu nasaba da ƙin jinin ƴan ci-rani. Fiye da ƴan Najeriya 260 ne suka isa Legas a ranar 11 ga watan Yuni. An samu jinkiri a tashin jirgin na biyu da aka sa ran ranar 15 ga Yuni. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar da dawowar wasu a safiyar yau.

Fitaccen jarumin fina-finau Kannywood, Saddiq Sani Saddiq, ya furta cewa babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta ya samo asali ne daga gwamnonin jihohi. Ya ce ana bai wa gwamnoni kuɗaɗe masu tarin yawa domin su karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da suke fuskanta. Ya kuma yi kira ga al’ummar Arewacin Najeriya da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu tare da zaɓen shugabannin da suka dace.

Jami’an ‘yan sanda biyu sun mutu yayin da rundunar ‘yan sanda ta ceto mutane tara daga hannun masu garkuwa da mutane a kusa da Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ne ya fitar da sanarwar. An kai samame bayan samun bayanan sirri, inda aka ceto mutanen tara da aka daure da igiya. Wasu da ake zargin masu garkuwa ne suka yi wa jami’an kwanton bauna a dawowarsu, inda jami’ai biyu suka mutu.

Hukumar Hisbah reshen ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina ta haramta shirya ko halartar bukukuwan Sign Out ga daliban ajin ƙarshe na sakandire. Jami’in sashen kula da kafafen sadarwa, Hamza Isya, ne ya fitar da sanarwar. Hukumar ta ce bukukuwan na tattare da rubuce-rubuce a jiki, kalamai marasa tarbiyya da cakuɗuwar maza da mata. Hisbah ta bukaci iyaye da malamai su sanya ido kan dalibai.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe wani sojanta a wani abin da ta bayyana a matsayin “aiki mai muhimmanci” a kudancin Lebanon. Duk da tsagaita wuta da aka sanar, ana samun rahotannin arangama tsakanin Isra’ila da dakarun Hezbollah. Wani mai magana da yawun sojojin Isra’ila ya shaidawa AFP cewa sojan ya mutu ne a lokacin da motar sa ta kife. Sojoji 37 da wani ma’aikaci farar hula sun mutu tun bayan fara rikici a farkon watan Maris.

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran da ta isa Amurka da safiyar yau ta gudanar da atisaye domin shirin tunkarar wasan da za ta yi da Masar ranar Asabar a filin wasa na Jami’ar Washington da ke Seattle. ‘Yan wasa 29 ne suka halarci atisayen. A gobe Juma’a ne tawagar za ta gudanar da wani atisaye a filin wasan. Wasan da za ta yi da Masar zai yanke hukunci kan makomar tawagar Iran a gasar cin kofin duniya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • YAHAYA SHUAIBU

    Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker