Labaran Rana Na Yau Jumaa 26 Yuni 2026 Hausa360

Saurari cikakken Labaran Rana Na Yau Juma’a 26 June 2026 Hausa360
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kai ziyara na musamman ga Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Kano. Kwankwaso tare da dan takarar gwamna na NDC a Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ne suka tarbi Obasanjo. Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan, ya tabbatar da ziyarar. Ya bayyana cewa ziyarar ta bai wa shugabannin damar gaisawa da tattaunawa cikin yanayi na sada zumunci, amma bai bayyana cikakken bayanin tattaunawar ba.
Hukumar EFCC da CAC sun kaddamar da wani mataki na hadin gwiwa domin dakile ayyukan masu gudanar da harkar POS da ba su yi rajista ba. Hukumomin sun yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya zama babbar barazana ga tsaron kasa da tsarin hada-hadar kudi. EFCC ta fara bincike kan wani mai canjin kudi (BDC) da Amurka ta kakabawa takunkumi. Shugaban CAC, Ibrahim Adah, ya ce kashi 20 cikin 100 ne kawai na masu POS suka yi rajista.
Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi jimamin rasuwar fitaccen lauya kuma jagoran APC a jihar, Sanata Anthony Ademuyiwa Adeniyi, SAN. Oyebanji ya bayyana rasuwar a matsayin abin takaici. Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Yinka Oyebode, ne ya fitar da sanarwar. Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ranar Laraba 24 ga watan Yunin 2026 yana da shekara 75 da haihuwa.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su cancanci sake samun dama ba, inda ya nace kan cewa ba su da hakkin ci gaba da rayuwa. Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Laraba, 24 ga Yuni 2026. Uba Sani ya ce dole ne a shafe ‘yan ta’adda baki daya, ya kuma jaddada cewa ayyukansu sun hana mutane da yawa cin moriyar rayuwarsu.
Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala karatun shekra uku na farko a Sakandare (BECE) inda jimillar dalibai 186,291 suka yi rijistar jarabawar a fadin kasar. Dalibai sun rubuta jarabawar ne a darussa 12 a jihohi 36 da FCT da kuma kasashen ketare guda biyar. An fara jarrabawar ne a ranar 20 ga Afrilu kuma an kammala a ranar 30 ga Afrilu, 2026. Kwamitin ya amince da ranakun 22 da 23 ga Yuli domin sake rubuta jarabawar a darussan lissafi da turanci.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bukaci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta duba yiwuwar sauya wasu shugabannin Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gwoza, FCE Gwoza, kan rashin fara karatu bayan shekaru. Gwamna Zulum ya nuna damuwa kan yadda kwalejin ta shafe kusan shekaru uku da kafuwa ba tare da fara ayyukan karatu ba. Gwamnatin Borno ta ware sama da Naira miliyan 200 domin fara aiki a kwalejin. Gwamnan zai tura rahoto ga ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Mataimakin shugaban kasar Amurka J.D. Vance ya ce Washington da Tehran sun amince da kafa wata hanyar sadarwa ta kai tsaye da dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) domin rage haɗarin sake barkewar rikici. A wata hira da UnHard, Vance ya ce tsarin zai hada da ganawa tsakanin jami’an sojojin Iran da na Amurka a Doha, Qatar. Iran za ta tura wani daga IRGC, Amurka kuma za ta tura wani daga CENTCOM domin warware bambance-bambance.
