Labaran Duniya

Yakin Iran Ya kara Amfani Da Motocin Lantarki

Rikicin da ke faruwa a kasar Iran ya haddasa karuwa sosai wajen amfani da motoci masu amfani da lantarki a kasashe daban daban na duniya.

Tashin farashin man fetur da ya biyo bayan rikicin ya sa mutane da dama suka fara komawa amfani da motocin lantarki domin rage kashe kudin mai da kuma samun sauƙin sufuri.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanonin kera motoci da dillalan sayar da ababen hawa sun samu karin bukata daga masu neman motocin lantarki, musamman a kasashen Turai da Asiya.

Wasu masana’antun sun bayyana cewa yawan masu neman irin wadannan motoci ya karu matuka tun bayan tashin farashin makamashi da rikicin ya jawo.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa rikicin Iran ya kawo cikas ga safarar mai a duniya, lamarin da ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi.

Hakan ne ya sa mutane da dama suka fara kallon motocin lantarki a matsayin mafita mai araha da kuma kariya daga yawan kudin mai da ake kashewa yau da kullum.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker