Labaran DuniyaWassanni

Filin Wasan Barcelona Zai Zama Makabarta

Barcelona za ta ba magoya baya damar ajiye tokar mamatan su a sabon filin wasa na Camp Nou daga ƙarshen 2027.

Kungiyar Barcelona ta sanar da wani shiri da zai mayar da filin wasanta na Camp Nou ya zama makabarta ga magoya bayanta. A karkashin shirin, magoya bayan da suka mutu za a iya ajiye tokarsu a cikin filin wasan. Kungiyar ta ce za ta samar da rumfunan jana’iza 26,000 domin magoya bayan da suke son kasancewa da alaka da kungiyar har abada.

Barcelona ta bayyana farashin wannan sabis. Fan da zai biya Yuro 2,490 zai samu shekaru 10. Wanda zai biya Yuro 4,990 zai samu shekaru 25. Wanda kuma zai biya Yuro 5,990 zai samu shekaru 50. Akwai karin kudin kulawa na Yuro 70 a kowace shekara.

An ce za a bude wannan makabartar ne a karshen shekarar 2027. Rahoton jaridar Le Parisien ce ta bayyana hakan. Wannan shiri wani bangare ne na aikin sabunta Camp Nou da Barcelona ke yi.

Wannan labari ya ma dadi ga magoya bayan Real Madrid, musamman a Najeriya. Dayawa sun ce Barcelona ta koma makabarta da gaske. Wasu sun ce wannan shine karshen darajar Barcelona. Magoya Madrid sun yi ta kwarkwasa kan lamarin a kafafen sada zumunta.

Wasu magoya Barcelona sun nuna rashin jin dadinsu kan shirin. Sun ce bai dace ba a mayar da filin wasa makabarta. Amma kungiyar ta ce shirin zai taimaka wa magoya baya su kasance da alaka da kungiyar har abada.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker