Siyasa

NDC Ta Amince Da Peter Obi Takara

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta bayyana Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban kasa guda daya tilo da ya samu amincewar kwamitin tantance yan takara kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar gabanin zaben shekarar 2027.

Peter Obi ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a yammacin ranar Talata tare da rakiyar Victor Umeh, inda ya gurfana a gaban kwamitin tantancewar karkashin jagorancin tsohon ministan ilimi, Sam Egwu.

Bayan kammala tantancewar, Sam Egwu ya bayyana cewa kwamitin ya gamsu da yadda Obi ya amsa tambayoyin da aka yi masa, tare da tabbatar da cewa ya cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar zabe suka tanada.

Ya kara da cewa kwamitin ya amince da Obi a matsayin wanda ya cancanci shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Daga nan ne aka miƙa wa Obi takardar shaidar tantancewa da kuma fom din tsayawa takara mai lamba 001.

Tun farko dai, Obi ya karɓi fom din nuna sha’awa da na takarar shugaban ƙasa a ranar 17 ga watan Mayu kafin wa’adin farko da jam’iyyar ta sanya.

Sai dai daga baya jam’iyyar ta sanar da kara wa’adin karɓar fom ga sauran masu neman takara zuwa ranar 24 ga watan Mayu.

Haka kuma, ta bayyana cewa za a fara karɓar cikakkun fom daga wadanda aka tantance tsakanin ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayu, yayin da ta jaddada cewa an rufe karɓar fom din takarar shugaban kasa gaba daya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker