Siyasa

Kwankwaso Ya Musanta Zargin Aiki Da Tinubu Sirri

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata zargin da ake yi masa cewa yana yi wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu aiki a boye.

Wannan martani na zuwa ne bayan mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature, ya yi zargin cewa Kwankwaso na taimaka wa Tinubu ta hanyar yin aiki tare da shi domin samun nasara a zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Sai dai Kwankwaso ya musanta wannan ikirari, yana mai cewa ba gaskiya ba ne kuma ba shi da wata alaka ta boye da za ta danganta shi da irin wannan zargi.

Ya bayyana cewa irin wadannan maganganu na siyasa ne kawai, wadanda ake yawan yi domin rikita jamaa da kuma haifar da rashin fahimta a tsakanin yan siyasa.

Ya kuma jaddada cewa yana mai da hankali ne kan harkokin jamiyyarsa da kuma batutuwan da suka shafi ci gaban kasa, ba wai wata hulda ta sirri da shugabancin kasa ba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker