Abdullahi Sule Ya Samu Tikitin Sanatan Nasarawa Ta Arewa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya samu tikitin takarar kujerar sanatan Nasarawa ta Arewa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress bayan kammala zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya samu cikakken goyon bayan wakilan jam’iyyar da shugabanninta a yankin, abin da ya ba shi damar lashe tikitin ba tare da wata matsala ba.
Nasarar tasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye shiryen babban zaben kasa mai zuwa, inda jam’iyyun siyasa ke tantance yan takararsu domin fafatawa a matakai daban daban.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa samun tikitin da Abdullahi Sule ya yi zai kara wa jam’iyyar APC karfi a yankin Nasarawa ta Arewa, musamman ganin irin tasirin da yake da shi a siyasar jihar.
Ana sa ran zai mayar da hankali wajen yakin neman zabe domin neman goyon bayan al’umma kafin gudanar da babban zaben.





