Duniya

Iran: Duk Wanda Ke Son Wucewa Ta Mashigar Hormuz Sai Ya Hada Kai Da Mu

Ma’aikatar tsaron kasar Iran ta bayyana cewa duk wata kasa ko jirgin ruwa da ke son wucewa ta mashigar Hormuz dole ne ya yi aiki tare da Iran.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, wadda kafofin yada labaran kasar suka wallafa, ta ce hanya guda tilo da kasashe da abokan huldarsu za su iya bi domin wucewa ta mashigar Hormuz ita ce ta hanyar haɗin kai da Iran.

Sanarwar ta kuma yi gargaɗi cewa duk wani yunkuri na kai hari kan gabar teku ko tsibiran Iran zai iya haifar da tsauraran matakai daga gwamnatin kasar.

A cewar ma’aikatar tsaron, idan aka kai wa Iran hari, za ta iya daukar matakin rufe hanyoyin ruwa da ke kaiwa gabar ƙasashen yankin Tekun Fasha ta hanyar dasa nakiyoyi a yankunan ruwan.

Sanarwar ta kara da cewa ba kawai mashigar Hormuz ba, har ma da sauran hanyoyin ruwa a yankin Gulf za su iya shiga cikin wannan mataki, tare da ɗora alhakin duk wani sakamako ga kasar da ta kai hari.

Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, inda manyan jiragen dakon mai ke wucewa kullum zuwa kasuwannin duniya. Duk wani tashin hankali a yankin na iya shafar kasuwancin mai da tattalin arzikin ƙasashe da dama.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker