Kiwon Lafiya
Trending

Hawan jini yayin juna biyu: Abubuwan da suka kamata a sani

Hawan jini yayin da mace ke da juna biyu ba lallai bane ya zama wani abu da ke da hatsari a ciki musamman idan aka ba shi kulawan da ya dace. Ga abubuwa da ya kamata mace ta sani domin ta kula da kanta da kuma jaririnta.

Yayin da mace ta san ta na da hawan jini a lokacin da ta ke dauke da juna biyu to ya kamata ta kasance a cikin kula na likitoci wato close monitoring ke nan a Turance.

Ire-iren hawan jini na masu ciki

Wani lokacin mace na kancewa ta na da hawan jini kafin ma ace ciki ya shige ta. Wasu lokutan kuma hawan jinin na samuwa ne lokacin da ta rigaya ta yi cikin, wato  bayan ta dauki cikin ke nan. Ga ire-iren hawan jinin masu ciki kamar haka:

  1. Gestational hypertension. Mata da ke da irin wannan hawan jini sukan same shi ne bayan sun dauki ciki da sati 20. Ba a samun furutin (protein) fiye da kima a fitsarinsu ko wani alamu na lalata wani daga cikin muhimman gabobin jikinsu (organ damage). Amma wasu mata masu dauke da wannan hawan jini na gestational hypertension ya kanyi tsanani sai su samu yanayinnan da ake kira da pre-ekalamsiya (preeclampsia).
  2. Chronic hypertension. Chronic hypertension wato hawan jini ne da ya tsananta wadda kuma yana nan ne a jikin mace kafin ma a ce ta sami juna biyu ko kuma kafin cikinta ya kai sati 20. Sabo da ita cutar hawan jini ba kasafai ta ke nuna alamunta ba, to yana da wuya a san lokacin da cutar ta shigi mutum.
  3. Chronic hypertension with superimposed preeclampsia. Wannan yanayi na faruwa ne ga matan da suke da chronic hypertension kafin shigan ciki wadanda suke fama da tsananin hauhawar jini (worsening high blood pressure) da kuma furutin a fitsarinsu ko kuma wasu matsaloli na daban da hawan jini ke kawo wa a lokacin juna biyu.
  4. Preeclampsia. Wannan yanayi na faruwa ne lokacin da hawan jini ya fara bayan sati 20 da daukar cikin mace. Sannan ana alakanta yanayin da alamun lalacewa da wasu gabobi masu muhimmanci suka yi. Gabobin sun hada da kamar su koda, hanta, jini da kuma kwakwalwa. Idan ba a yi jinyar wannan preeclampsia ba zai iya haifar da matsaloli ga uwa da kuma jaririnta. Wannan matsala kan iya kaiwa mace ta fara fisge-fiske ko kuma seizure wato ta shiga yanayin da ake kira da eclampsia ke nan.

A da can baya, akan sami mace da preeclampsia ne idan mace na da hawan jini sanan kuma tana da furutin a fitsarinta. Yanzu masana sun gano cewa mace na iya samun preeclampsia ko da ba a sami furutin a fitsarinta ba.

Mene ne ya sa samun hawan jini lokacin da mace ke dauke da juna biyu ya ke da hatsari?

Hawan jini yayin da mace ke da ciki na iya kawo hatsarurruka da dama, wasu daga cikin irin wadannan hatsarurrukan sun hada da:

  1. Rage gudun jini zuwa mahaifa. Idan mahaifa ba ya samun isashen jini, to yawan iskan oxygen da kuma nutrients (abinci masu gina jiki) da jariri ke iya samu na iya raguwa. Wannan matsala na iya haifar da jinkirin girman jariri (slow growth), ko nauyin jariri ya ragu (low birth weight) ko kuma haihuwan jariri kafin lokacinsa. Haihuwan jariri kafin lokacinsa kuma na iya kawo matsalar numfashi, da infection da wasu matsalolin na daban ga jaririn.
  2. Fashewar mahaifa. Preeclampsia yana kara hatsarin da mahaifa ke rabuwa daga mazaunar shi a yutarus (uterus) kafin lokacin haihuwa. Idan rabuwan ya yi tsanani yana haifar da zuban jini mai yawa wadda zai iya sa mahaifiya ta rasa ranta ko na jaririnta.
  3. Intrauterine growth restriction. Hawan jini na iya haifar da rage girman jariri ko abinda ake kira a turance da suna intrauterine growth restriction.
  4. Rauni ga sauran sassan jiki (organs). Idan ba a kula da hawan jini da kyau ba ya kan iya haifar da rauni ga kwakwalwa, da zuciya, da huhu, da koda, da hanta da ma wasu daga cikin manya-manya sassan jiki. Idan abin ya yi tsanani ya kan iya daukan rai.
  5. Haihuwa kafin lokacin da ya dace. Wani lokaci haihuwa kafin lokaci wani hanya ne da ake bi domin samun kariya daga hatsarin da cutar hawan jini kan kawo.
  6. Samun cutar da ta shafi zuciya nan gaba (future cardiovascular disease). Idan mace ta taba samun preeclampsia to ta kan iya shiga hatsarin samun ciwon zuciya da cutar hanyar jini a nan gaba. Sannan hatsarin na karuwa idan mace ta sami preeclampsia fiye da daya ko kuma ta taba haihuwa kafin lokaci saboda hawan jini.

Yaya mace za ta san ta kamu da hawan jini yayin da ta ke dauke da juna biyu?  

Gwajin BP (blood pressure) na daga cikin abubuwan da ake yi wajen kula da mace mai ciki. Idan aka sami mace da chronic hypertension to malaman jinyarta za su bada umarnin yin gwajin hawan jini. Ana iya daura mace a daya daga cikin wadannan matakai na hawan jini:

  1. Elevated blood pressure
  2. Stage 1 hypertension
  3. Stage 2 hypertension

Bayan sati ashirin da shigan ciki, idan aka sami mace da BP da ya wuce 140/90 mm Hg sama da karo biyu kuma a tsakanin gwaji da gwaji ana bada ratan awa 4 haka nan sannan babu wani rauni a wani sassan jiki (organ damage) to wannan shi ne ake kira da gestational hypertension.

Yaya mace za ta san ta sami preeclampsia?

Baya ga hauhawan jini, wasu daga cikin alamun preeclampsia sun hada da:

  1. Yawan furutin a cikin fitsari ko kuma wasu alamu na ciwon koda
  2. Ciwon kai mai tsanani
  3. Canji a gani (vision), har ya kai ga rasa gani na wani lokaci, ko kuma ganin duhu-duhu, ko kuma rashin jin dadin gani a cikin haske
  4. Ciwon ciki yawanci ta kasa da hakarkari ta gefen dama.
  5. Tashin zuciya ko amai
  6. Raguwan yawan yin fitsari
  7. Samun matsalar wajen aikin hanta
  8. Nufashi sama-sama saboda ruwa da ke cikin huhu
  9. Raguwar yawan sinadarin platelets (wani sinadari ne mara kala da ke dauke da cells na jini) a cikin jini

Kiba da kumburi cikin lokaci guda, akasari a fiska da hannu, yawanci sukan biyo bayan preeclampsia. Amma dai wannan alamun na kiba kan faru a yawancin lokuta ga mace mai juna biyu saboda haka alamun kiba da kumburi ba lallai ba ne su zama alamun preeclampsia.

Shin shan maganin hawan jini lokacin da mace ke da juna biyu babu illa?

Idan mace na da hawan jini a lokacin da take da juna biyu to lallai kar ta yi garajen shan magani sai wadda kwararren likita ya rubuta ma ta. Domin shi likitan ya san irin yanayin da ta ke ciki kuma ya yi la’akari da duk wani hatsarin da ka iya aukuwa kafin ya bata wannan maganin.

Mene ne mace mai hawan jini za ta yi kafin shigan ciki?

Idan mace na shirin daukan ciki kuma tana da hawan jini to yana da kyau ta shirya ta je ta ga likita wato preconception appointment. Ta gana da family doctor dinsu ko kuma cardiologist, za su dubata sannan wata kila su bata shawaran irin canji da ya kamata ta yi na jinya kafin daukan cikin.

Idan mace na da kiba sosai wata kila likitan zai bata shawaran rage wannan kibar kafin ta gwada daukan ciki.

Abubuwan da za a yi wa mace mai hawan jini lokacin ciki

  1. Duba nauyi da BP a duk lokacin da ta ziyarci likita
  2. Gwajin jini da kuma fitsari akai-akai
  3. Yawan yin gwajin ultrasound domin kula da lafiyan jariri
  4. Gwajin fetal heart rate domin kula da lafiyan jariri
  5. Likita na iya umurtar mace da ta kula da motsin jaririnta a kullum

Mene ne zan yi domin kariya daga irin matsalolin da za su iya afkuwa?

  1. Ziyartar likita akai-akai ba fashi (prenatal appointment)
  2. Shan maganin hawan jini kamar yadda likita ya umurta
  3. A kasance ana motsa jiki kamar yadda ya kamata (stay active)
  4. Cin abinci masu lafiya (healthy diet)
  5. Sanin abubuwan da ko da wasa ba za’a yi ba, kamar su shan giya, kwaya da makamantansu

Lokacin nakuda da haihuwa

Likitoci na iya bada shawarar bada magani domin a tada nakuda kafin lokacin haihuwa ya yi (induced labor). Likitoci sun san lokacin da ya dace a yi wa mace induction din bayan sun tabbatar hatsari ya ragu.

Shayarwa ga mace mai hawan jini

Ana bawa yawancin mata masu hawan jini kwarin guiwar sosai na shayar da jariransu zallar nono ko da kuwa suna shan magani ne. Amma kafin mace ta haihu yana da kyau ta yi magana da likita akan ko da akwai wani canji da za a yi mata na maganin da ta ke sha na hawan jinin domin shayarwa.

Daga karshe, kamar kullum kar ku manta muna kawo muku ire-iren wannan makala ne domin karuwan ilimi da kuma wayar da kai. Idan mutum na fama da ciwo ko ya ga wani alamu na ciwo, to likita shi ne kadai zai duba ka kuma ya baka magani. Allah Ya mu lafiya da zaman lafiya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Ta
Bakandamiya Kiwon Lafiya
Tushi
Hawan jini yayin juna biyu
Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker