Ba komai ya jawo fetur ya yi wahala ba illa yankewar kaya daga kamfanin mai na kasa watau NNPCL a ‘yan kwanakin nan
‘Yan kasuwa sun tabbatar da haka, kuma sun ce an yi zama tsakaninsu da kamfanin domin ganin matsalar ta zo karshe. Idan komai sun zo daidai, da zarar an gama sauke mai a birnin Warri, layin motoci da babura za su bace a gidajen mai a kasar.