Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da sarkin Misau
Gwamna Bala Muhammad ya amince da dakatar da Me Martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmad Suleiman.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin bincike kan rikicin da ya afku a Zadawa dake karamar hukumar Misau da yayi sanadiyar rasa rayuka.
Yayin kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati, Gwamna Bala Muhammad yace matakin dakatar da Sarkin, shugaban karamar hukumar da kuma wasu shugabannin yankin ya zama wajibi don bada kwamitin damar bincike da kuma zama izina ga masu zagon kasa ga zaman lafiya a jihar Bauchi.
Yayin taron, Gwamna Bala Muhammad ya rantsar da sabon shugaban rikon karamar hukumar Honorable Isah Kufai tare da kiransa da yayi aiki da kwamitin da aka kafa don lalubo musabbabin rikicin.
A cewar Lawal Muazu Bauchi me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani.