LabaraiTsaro

Mutun Takwas sun shiga komar hukuma kan zargin kashe ‘yan sanda a Delta

An kashe ƴan sandan ne a wani harin kwanton-ɓauna da aka kai musu a lokacin da suke hanyar zuwa aikin ceto.

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta sanar da kama mutum takwas waɗanda ake zargi da hannu a kashe jami’anta shida a dajin Ohoro da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli North a Jihar Delta.

Mai magana da yawun ƴan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce a halin yanzu waɗanda ake zargin suna hannu kuma ana gudanar da bincike a kansu.

Ya bayyana cewa sun yi nasarar kama mutanen da ake zargin bayan gudanar da bincike mai zurfi, inda ya ce tun can dama an kama mutum biyar jim kaɗan bayan kashe jami’an ƴan sandan, sai kuma sauran ukun aka kama su a wurare daban-daban.

An kashe ƴan sandan ne a wani harin kwanton-ɓauna da aka kai musu a lokacin da suke hanyar zuwa aikin ceto.

Ƴan sandan da aka kashe sun haɗa da Inspector Abe Olubunmi da Inspector Friday Irorere da Sergeant Kuden Elisha da Sergeant Akpan Aniette da Sergeant Ayere Paul da kuma Sergeant Ejemito Friday.

Rundunar ƴan sandan ta kuma jaddada cewa za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin ganin an hukunta duka waɗanda suke da hannu a kashe jami’an nata.

Jihar Delta ta fuskanci rikice-rikice a baya-bayan nan musamman kan batun kashe jami’an tsaro inda ko a ranar 14 ga watan Maris ɗin nan sai da aka kashe sojojin Nijeriya 17 a jihar.

Wannan lamarin ya tayar da hankalin jama’ar ƙasar inda a nasu ɓangaren su ma sojojin ƙasar suka lashi takobin zaƙulo waɗanda suka kashe jami’an nasu tare da hukunta su.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker