DuniyaLabarai

Jami’o’in Turkiyya sun goyi bayan zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a jami’o’in Amurka

Wata sanarwar hadin gwiwa da jami'o'i 16 suka fitar ta bayyana cewa, matakin da hukumomi ke ɗauka a kan zanga-zangar lumana da daliban jami'o'i a Amurka ke yi, "take 'yancin ɗan'adam ne da 'yancin karatu.

Jami’o’i da dama na ƙasar Turkiyya sun nuna adawa a kan amfani da ƙarfi da ake yi a kan ɗaliban da ke zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawan Gaza a faɗin Amurka.

Jami’o’in na ƙasar Turkiyya sun fitar da sanarwar goyon bayan ɗaliban da ke zanga-zangar — wacce aka fara ta kwanaki kaɗan da suka wuce a Jami’ar Columbia a Amurka, ta kuma yaɗu zuwa jihohi daban-daban — sannan sun yi kakkausar suka ga yadda ƴan sanda ke cin zarafin ɗaliban.

“Fiye da wata shida, ana amfani da ƙarfi a kan ɗaliban jami’a waɗanda suke zanga-angar lumana don nuna adawa ga ayyukan cin zalin da ake yi wajen lalata rayuwar mutanen da ke zaune a Gaza,” kamar yadda sanarwar ta haɗin gwiwa daga jami’o’i 26 ta bayyana.

Jami’o’in Turkiyya sun jaddada ƙorafin cewa “An yi amfani da matakin da bai dace ba kan zanga-zangar lumana da ɗaliban jami’a suka yi a matsayin wani abu ne na ‘yancin ɗan’adam da ‘yancin karatu, kuma muna matukar nuna takaicinmu tare da yin Allah wadai da hakan.”

Sun yi nuni da cewa har an tsare wasu ɗalibai, kuma jami’o’in sun zaɓi sauya salo zuwa karatu daga nesa duk don dakatar da zanga-zangar.

Tun daga Jami’ar Columbia zuwa Yale, Jami’ar New York zuwa Harvard, masu zanga-zangar suna neman jami’o’insu su goyi bayan kiran tsagaita wuta a Gaza tare da yanke hulda da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila.

Yakin da Isra’ila ta yi a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, wanda yanzu ya shiga kwana na 202, ya kashe Falasdinawa akalla 34,262 – kashi 70 cikin 100 jarirai ne da yara da mata – tare da jikkata sama da mutum 77,229.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker