Duniya

Iran Ta Yi Gargadi Kan Yiwuwar Harin Bankunan Amurka da Isra’ila a Gabas ta Tsakiya

Iran ta yi barazanar kai hare-hare kan bankunan Amurka da na Isra’ila da ke yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin martani ga abin da ta ce wani hari ne da aka kai kan wani banki a cikin kasar.

Mai magana da yawun rundunar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babban kwamitin hadin gwiwar sojin Iran, Ebrahim Zolfaghari, ya bayyana cewa Iran za ta iya kai hari kan cibiyoyin tattalin arziki na Amurka da Isra’ila a yankin.

Zolfaghari ya gargadi jama’a a yankin da kada su kusanci bankuna daga nisan kilomita daya, yana mai cewa hakan na iya zama matakin kariya idan aka fara kai hare-hare.

Ya ce, “Abokan gaba sun ba mu damar kai hari kan cibiyoyin tattalin arziki da bankuna da Amurka da Isra’ila ke da su.”

Rahoton gidan talabijin na gwamnatin Iran IRNA ya bayyana cewa an kai hari kan wani gini na Bankin Sepah, wanda bankin gwamnati ne da ke birnin Tehran.

Haka kuma, a ranar Talata kafafen watsa labaran Iran sun ce an samu wasu matsaloli a ayyukan Bankin Sepah da kuma wani bankin gwamnati mai suna Bankin Melli, lamarin da ya shafi gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker