Iran Ta Ki Yanke Shawara Kan Tattaunawa da Amurka

Har yanzu Iran ba ta bayyana matsayarta kan ko za ta halarci tattaunawar da Amurka a Pakistan ba, duk da cewa saura kwana guda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu ta ƙare.
Hukumomin Tehran ba su tabbatar da tura tawaga ba, yayin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance, wanda ake sa ran zai jagoranci tawagar Amurka, har yanzu bai bar Washington ba.
A nasa ɓangaren, Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ba za ta ɗage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin Iran ba har sai an cimma yarjejeniya mai gamsarwa.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka na son a sake buɗe mashigar Hormuz tare da kuma Iran ta miƙa sinadarin uranium ɗinta. Sai dai Iran ta yi watsi da wannan buƙata, tana mai cewa ba za ta amince da irin wannan shiri ba.
Shugaban tawagar tattaunawar Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya jaddada cewa ƙasar ba za ta shiga wata tattaunawa ƙarƙashin matsin lamba ba.




