Siyasa

Gwamnan Kano Ya Mika Sunan Murtala Garo a Matsayin Mataimakin Gwamna

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Alhaji Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin Mataimakin Gwamna.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan naɗin ya yi daidai da sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya bai wa gwamna damar naɗa Mataimakin Gwamna idan gurbi ya samu.

Mukamin ya zama babu kowa ne bayan murabus ɗin da tsohon Mataimakin Gwamna, Kwamared Abdussalam Gwarzo, ya yi da kansa a ranar 27 ga Maris, 2026.

Bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, Gwamnan ya roƙi Majalisar Dokokin Jihar da ta gaggauta ba da amincewa ga wannan naɗi.

Alhaji Murtala Sule Garo mai shekaru 48, gogaggen ɗan siyasa ne kuma mai kwarewa a harkokin mulki, inda ya shafe sama da shekaru ashirin yana aiki a mukamai daban-daban, na zaɓe da kuma na naɗi.

Ya taɓa rike mukamin Sakataren Tsare-tsare na Jiha a jam’iyyarsa, mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara na musamman, da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo da aka zaɓa.

Haka kuma, ya taba zama Shugaban ALGON na Jihar Kano, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, sannan kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Naɗin nasa na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa tsarin mulki da kuma tabbatar da ingantaccen gudanar da ayyuka a Jihar Kano.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker