IlimiLabarai

Fasa runbun abincin tallafi na COVID19 ba daidai bane inji malamin addini

Babban Malamin addini mai suna Dr. Ibrahim Jalo Jalingo yayi kira da al’umma a kan fasa runbun da aka ajiye kayan tallafi na COVID19 akan hakan ba dai dai bane.

Dr. Jalo yayi kira da gwamnati ta dauki matakin gaggawa game da hakan, Malamin yayi wannan rubutu ne a shafin sa na yanar hizo a jiya asabar bayan fashe fashen runbun ajiye kayan abinci da akayi a wasu sassan jihohin Nigeria.

Ga abin da ya rubuta a shafin sa na yanar gizo

  1. Cikin ‘yan awowi kadan da suka wuce mutane sun yawaita tambayar mu game da fasa ma’ajiyar abinci na taimakon Corona da aka a wasu jihohi, da kuma diban abincin, ko saye a hannun wanda ya diba.
  2. Amsarmu ga masu wannan tambayar ita ce dukkan abin da aka tambayar ba daidai ba ne musulmi ya yi shi: Kada ku fasa shagunan gwamnati, kada ku dauki abincin da aka ajiye a cikin shagunan, kada ku saya ko ku sayar da irin wannan abincin.
  3. Lalle bin doka da oda yana daga cikin abin da zai tabbatar wa al’umma babbar maslaharsu da kuma maslahar kasarsu.
  4. Sannan muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin gyara inda suka yi kure domin samar wa Kasa da talakwan kasa mafita mai kyau.
  5. Allah ya taimake mu.
Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker