DuniyaRayuwa

An Ceto Wani Mutum Da ‘Yan Uwansa Suka Daure Shi Na Tsawon Shekaru 30 A Jihar Kano

An Ceto Wani Mutum Da ‘Yan Uwansa Suka Daure Shi Na Tsawon Shekaru 30 A Jihar Kano

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun ceto wani mutum mai shekaru 55 da ‘yan uwansa suka daure na tsawon shekaru 30 sakamakon yana da tabin hankali. Kamar yadda wani dan kare hakkin bil adama ya bayyana cewa mutumin ya shafe shekaru yana cikin wahala, inda aka daure shi jikin wani katon karfe a cikin wani daki da bai da kofa ko kuma taga.

Hakan ya sa ya fada wa ‘yan sanda halin da mutumin yake ciki bayan ya samu labari kan mutumin, kuma suka ceto shi tare da ‘yan sanda a garin Rogo da ke Kano.

“Mutumin yana da taɓin hankali kuma ya fara faɗa, a maimakon a nemo masa magani tun a 1990, sai mahaifinsa ya yanke shawarar ɗaure shi,” in ji Shu’aibu.

Bayan mahaifin mutumin ya rasu a shekarun baya, sai ‘yan uwansa suka ci gaba da kulle mutumin, amma a halin yanzu, an sake shi. Wasu daga cikin makwaftansa da suka san halin da yake ciki sun taimaka wurin ceton, in ji shi.

Mutumin mai shekaru 55 a halin yanzu yana babban asibitin garin Rogo inda a nan ne yake karɓar magani, inda kuma tuni aka tafi da ‘yan uwansa wurin ‘yan sanda.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin kuma ya ce ana gudanar da bincike.

Wannan ne aikin ceto na uku cikin kasa da makonni biyu da aka yi na mutane masu buƙata ta musamman da ‘yan uwansu suka yi musu ɗaurin talala.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker