LabaraiWasan Kwaikwayo
Adam A Zango ya roke Falalu A dorayi da ya sake film na Basaja
Fitaccen Jarumin masana’antar Kannywoood ya roke babban darekta Falalu a dorayi da ya sake film din Basaja.
Sai dai a wani zantawar da Jarumin yayi da BBC Hausa acikin shirin Daga Bakin Mai Ita yace shirin da yafi so shine Basaja kuma shine wanda masoya suke magana akai wanda dinbin masoya suke ta rokon sa da ya sake shirin Basaja.
Saidai jarumin yace shi kawai jarumine a cikin shirin da kuma direkta. Yace shirin na abokin aikin sa ne waton Falalu a dorayi, hakan yasa fitaccen Jarumin Wato Adam A Zango yake rokan Falalu A Dorayi da ya kammala shirin domin a sake wa masoya su kalla, domin kuwa ba’a gama dauka shirin ba, wata kil sai an fita kasar waje.
Ga cikakken hiran kamar yanda sukayi da BBC Hausa.