Adam A Zango : Babban Burina a Duniya Shi Ne Na Aure Mace Ta Gari
A hirar da BBC ta wallafa a cikin shirin Mahangar Zamani tare da Adam A. Zango, shahararren mawaki, jarumi, kuma jigo a Kannywood, ya bayyana cewa babban burinsa a rayuwa shi ne auran mace ta gari sannan ya nuna rashin jin dadinsa akan mumunar fahimtar da mutane suke yi masa na auri saki.
A dalilin haka ne, ya ja hankalin mutane a kan yarda da kaddara, ya kara da cewa komai ya faru mukaddari ne daga Allah, ciki harda rabuwa da matayensa da ya yi.
A cikin tattaunawarsa da Madina Dahiru Maishanu, jarumin ya bayyana dalilin da yasa aka ji shiru a kansa har na tsawon shekara biyu, inda yake cewa girma ne ya sa hakan, sannan kuma ahalinsa suna da bukatar lokacinsa.
Bayan haka akwai kalubale da jarumin ya tabbatarwa da duniya cewa ya hadu dasu a masana’antar Kannywood, daga ciki akwai matsaloli da ya samu da wasu masu shirya fina fanai da jarumai, sannan matsalar sa da iyalin sa. Kamar yadda ya bayyana, ya ce wadannan abubuwa su suka janyo ya ke ganin komai ya rikece masa, hakan ya sa ba ya iya maida hankali ko yayi tunanin abinda ya dace.
Hakan ya sa ya ce ya kamata ya dan koma gefe ya huta, ya samu nutsuwa daga cutar damuwa da ya ke ciki. Amma a halin yanzu mawakin ya fitar da wani sabon album dinsa mai taken “Babu Lokaci” wanda ya hada da wakokin kalangu, da na zamani, da na soyayya, harma da na Ingausa.
Daga cikin matsaloli da suke Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana abinda yafi yi masa ciwo a rai, inda yake cewa rashin hadin kai da rashin sanya jarumai da suka fi dacewa su taka rawa a shiri sai bin son zuciya su suka fi kona masa rai.
Daga karshe ya kara da cewa kaso tamanin cikin dari na ‘yan matan da suke shigan harkar fim, iyayensu basa so.