
Gwamnan jihar Borno a Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara zuwa garin Askira-Uba domin nuna alhini da jajanta wa iyalan daliban da yan ta’addan Boko Haram suka sace.
Wannan ziyara ta biyo bayan harin da aka kai ranar Juma’ar makon da ya gabata, inda aka yi awon gaba da sama da dalibai 40 daga yankin.
A yayin ziyarar, gwamnan ya tattauna da iyaye da shugabannin al’umma tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin ganin an ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda hare-haren ta’addanci ke ci gaba da jefa jama’a cikin damuwa da rashin tsaro a wasu sassan jihar.
Haka kuma, ya karfafa jami’an tsaro da su ƙara himma wajen bin sawun maharan tare da tabbatar da tsaron makarantu da sauran al’ummomi domin hana sake aukuwar irin wannan lamari. Mazauna yankin sun yaba da ziyarar gwamnan, suna mai cewa hakan ya nuna gwamnati na tare da su a wannan lokaci mai cike da jimami.





