Labarai
Yan Ta adda Sun Lalata Gonaki A Filato

Wasu batagari sun lalata amfanin gona a gonakin noman rani da ke yankin Zobwo a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau State.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin na kunshe cikin wata sanarwa da Weyi Agara ya fitar a madadin manoman yankin a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin amfanin gonakin da aka lalata akwai kabeji, masara, doya, wake, barkono da sauran kayan gona da al’umma ke dogaro da su domin samun abinci da kuɗaɗen shiga.
A cewar manoman, barnar da aka yi ta jefa su cikin mawuyacin hali tare da haifar da barazana ga samar da abinci a yankin.
Sun kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kamo waɗanda ake zargi da hannu a lamarin domin gurfanar da su a gaban doka.





