Labarai

Magoya Bayan Zaura Sun Bukaci APC Ta Tsayar Da Shi

Dubban magoya bayan Abdulkarim Abdullahi Zaura sun gudanar da gagarumin tattaki a cikin birnin Kano domin nuna goyon bayansu gare shi tare da bayyana rashin jin dadinsu kan rade-radin da ke cewa jam’iyyar APC ba za ta tsayar da shi takarar Sanatan Kano ta Tsakiya ba a zaben 2027.

Tattakin wanda hadakar kungiyoyin magoya bayan A.A. Zaura suka shirya ya jawo hankalin al’umma, inda aka ga dimbin mabiyansa suna yawo a manyan titunan Kano suna dauke da alluna da sakonnin nuna goyon baya ga dan siyasar.

Jagoran kungiyoyin A.A. Zaura, Jafar Abdullah, shi ne ya jagoranci tattakin tare da dubban magoya bayan da aka kiyasta sun kai kusan mutum 10,000.

Mahalarta tattakin sun fara gangamin ne daga filin sukuwa kafin su ratsa wasu manyan hanyoyi domin isar da sakonsu ga shugabannin jam’iyyar APC.

Da yake jawabi yayin tattakin, Jafar Abdullah ya bayyana cewa al’ummar Kano ta Tsakiya suna tare da A.A. Zaura dari bisa dari, kuma suna ganin shi ne mutumin da ya dace ya wakilce su a Majalisar Dattawa.

Ya kara da cewa Abdulkarim Abdullahi Zaura ya dade yana taimakawa jama’a musamman marasa karfi, duk da cewa bai taba rike wani mukamin gwamnati ba.

A cewarsa, irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’umma ne ya sa mutane da dama suke son ganin ya samu damar tsayawa takara.

Rahotanni sun nuna cewa wannan gangami na zuwa ne a lokacin da siyasar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya ke kara daukar zafi, musamman bayan da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ya mika fom dinsa na neman takarar kujerar a karkashin jam’iyyar APC.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan tattaki wata alama ce da ke nuna yadda fafatawar neman tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya ke kara tayar da kura a tsakanin ‘yan jam’iyyar da kuma magoya bayansu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker