Tashin Hankali a Teku: Iran Ta Kai Hari Kan Jirgin Mai na Amurka a Bahar Rum
Rahotanni daga gidan talabijin na gwamnatin Iran sun bayyana cewa dakarun rundunar ruwa ta kasar sun kai hari kan wani jirgin daukar man Amurka a safiyar yau a arewacin Bahar Rum, lamarin da ke kara tayar da hankalin duniya a yayin da rikici ke kara tsananta tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila.
A cewar sanarwar da aka karanta a tashar talabijin ta gwamnatin Iran, rundunar sojin juyin juya hali ta kasar, IRGC, ta ce an harba makami mai linzami kan jirgin.
Sanarwar ta ce: “Jirgin daukar man ya sha harbi da makami mai linzami a arewacin Bahar Rum, kuma har yanzu yana ci da wuta.”
Rundunar ta kuma bayyana cewa tana da “cikakken iko” da mashigar tekun Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar man fetur a duniya, domin tana hada yankin Gabas ta Tsakiya da Tekun Indiya.
Sai dai har yanzu babu cikakken tabbaci daga majiyoyi masu zaman kansu game da harin. Duk da haka, kungiyar kula da harkokin tsaron jiragen ruwa ta Biritaniya (UKMTO) ta tabbatar da cewa an samu wani hari kan jirgin ruwa a yankin.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke karuwa a Gabas ta Tsakiya, yayin da Iran ke takun saka da Amurka da Isra’ila kan wasu hare-hare da rikice-rikice da suka shafi yankin.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa duk wani hari kan jiragen mai a wannan yanki na iya kara tayar da hankalin kasuwannin mai na duniya tare da jefa zirga-zirgar jiragen ruwa cikin barazana.




