Wannan sanarwan mun samu daga wurin mai daukan tafsirin a kowane shekara Usman Shuaibu Kunsal (Mai Kasuwa) wanda ya shaida mana cewa Sheikh Dahiru ya sanar da manema labarai cewa
” Ansamu matsaya gameda Tafsirin bana wanda aka sabayi a Kaduna duk Shekara cikin zantawa da maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A yayi da maneman labarai a yau Laraba “
” Shehu ya bayyana cewa Insha Allahu a bana za’a gudanar da Tafsiri ne a Bauchi ba tareda Anje Kaduna ba Shehu ya kara da yace za’a turo masu daukan tafsirin daga Kaduna da Sauran wurare daban daban Inda zasu dauki Tafsirin a watsa a duniya”
Sannan Shehu yaja hankalin cewa kar’a daina Sallar Juma’a Akalla mutum goma Sha biyu, shima Sallan tahajudi da Asham A samu koda mutum bakwai zuwa sama a dunga gudanarda Sallah
Shehu yace Ayi hakurida yanda Allah ya kaddara lamarin Allah yabamu lafiya da zaman lafiya albarkan Manzon Allah S.A.W