Duniya
Trending

Saudiyya sun dakatar da yin sallah a jam’i a fadin kasar.

Mutane 133 aka tabbatar sun kamu da cutar a Kasar Saudiyyan

Hukumomi a Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, idan ban da masallacin Ka’abah da kuma na Madina waton Masallacin Manzon Allah sira da amincin Allah su tabbata agareshi, a cewar kamfanin dillacin labaran kasar wato Saudi Gazette.

A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji shiga kasar saboda yaduwar cutar coronavirus.

An dauki matakin ne makonni kadan kafin azumin watan Ramalana inda Musulmi kan yi tururuwa zuwa kasar domin gudanar da ayyukan ibada.

Kawo izuwa yanzu, mutane 133 aka tabbatar sun kamu da cutar a Kasar Saudiyyan.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker