Labarin wata budurwa mai tare da abin al’ajabi
Wata budurwa ce saurayinta ya zo gunta hira, suna cikin hira sai ya yanke jiki ya fadi gawa.
Abu ya dami budurwar domin sun yi maganar aure da shi lokaci suke jira kawai. Sai ‘yan uwan saurayin suka ce ita ta kashe shi ba za su yadda ba, kawai aka mata sharri ta yi kisan kai, aka je kotu alkali ya yanke mata hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Bayan ta shiga gidan yari, ba ta da wani aiki sai kuka. Ana nan sai wani mutum da yake aiki a gidan, shi aikinsa kawai idan mutum ya rasu (mutu) ya zo ya yi dawainiyar sanya mamacin a akwati a rufe shi. Sannan aje a bunne gawar.
Kullum sai ya ganta tana kuka har sai wataran ya je ya tambaye ta, ta kwashe labari ta gaya masa, tace kuma kukan da take yi kawai ba don komi ba, sai saboda tana budurwarta amma za ta kare rayuwarta a gidan yari ba tare da ta yi aure ba. Ko yaushe ya shigo sai ya zo wajenta su gaisa yana dai dan debe mata kewa, har soyayya ta shiga tsakaninsu sosai har suna maganar aure kuma suna tabbatar wa juna da cewa ba wanda ya isa ya raba su. Sai dai kuma ta yaya za su yi aure?
Wata rana suna hira sai ta ce ya kamata mu san yadda za mu yi na kubuta mu je mu yi aure sai ya ce mata to ya za a yi? sai ta ba da shawara cewa Idan an sake mutuwa a gidan za ta je ta shiga cikin akwatin da gawar take. Idan ya zo shi da yaransa sai ya rufe kawai. idan aka binne su sai ya je daga baya ya tone ta sai su gudu. Sai ya amsa yace to, haka za a yi, kawai idan anyi rasuwa kije ki shiga.
Bayan kwana biyu da magariba aka yi rasuwa a gidan yarin kawai ta tashi ta gano inda gawar take ba tare da ta nemi inda yake ba tun da dama da alkawarin, kawai sa ta dauki wata ‘yar karamar touch light ta tafi dakin da gawar take ta je ba tare da dubawa ko mace ce ko namiji ba gawar kawai ta kwanta kusa da ita a cikin akwatin. TOFA yaransa na zuwa suka rufe suka tafi suka je suka binnesu suka dawo prison.
Wohoho…! Ta dan jira kadan ba ta ji ya zo ya tone ta ba sai ta fara cewa a zuciyarta (ashe dai ya ki zuwa ya tone ni tab!) Sai ta ce bari dai na duba gawar nan namiji ne ko mace sai ta zaro touch light din nan ta yi yan dabaru ta haska fuskar gawar, kwatsam sai taga Ashe Saurayin nata ne wanda suka yi zai tone ta, ashe shi ya rasu.