Labarai

Kotu Ta Ba ICPC Damar Ci Gaba da Tsare El-Rufai Na Karin Kwanaki 14

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, ICPC, ta bayyana cewa kotu ta ba ta izinin ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, na tsawon karin kwanaki 14.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun ta amince da bukatar hukumar ne domin ta samu isasshen lokaci na kammala binciken da take yi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da wasu laifuffuka da ake zargin tsohon gwamnan da aikatawa.

Rahotanni sun ce an bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis a gaban lauyan El-Rufai, kuma wa’adin zai kare a ranar 19 ga watan Maris, kamar yadda ICPC ta bayyana.

Sai dai lauyan tsohon gwamnan ya shigar da kara a Babbar Kotun Majistare ta Bwari da ke Abuja, yana neman a soke umarnin tsarewar. Ya gabatar da hujjoji da dama, yana mai cewa ba a bi ƙa’ida ba wajen tsare El-Rufai.

Duk da haka, kotun ta bayyana cewa har yanzu akwai buƙatar a ci gaba da tsare shi har sai an kammala binciken da ake yi.

Babban Mai Shari’a na Kotun Majistare, Okechukwu John Akweke, ya sanya ranar 17 ga watan Maris domin yanke hukunci kan ko za a soke sabon umarnin tsarewar ko a’a.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker