Wassanni
Kano Pillars Ta Jinjinawa RFI Hausa Kan Goyon Baya

Kungiyar wallon kafa ta Kano Pillars ta bayyana godiya da jin dadinta ga RFI Hausa bisa irin gudunmawar da kafar yada labaran ta bayar yayin kakar wasannin da aka kammala a ranar Lahadi.
Kungiyar ta ce RFI Hausa ta taka muhimmiyar rawa wajen yada labarai da shirye shiryen da suka taimaka wajen bunkasa harkokin kwallon kafa tare da kara kusantar masoya kungiyar da abubuwan da ke faruwa a kakar wasan.
Haka kuma, Kano Pillars ta yaba da yadda kafar yada labaran ke nuna goyon baya ga wasannin cikin gida, tana mai cewa hakan na karfafa gwiwar yan wasa da magoya baya gaba daya.





