Wassanni

Atletico ta fitar da Barcelona daga Gasar Zakarun Turai

Atletico Madrid ta tsallaka zuwa wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai bayan ta fitar da Barcelona da jimillar ƙwallaye 3-2, duk da cewa an doke ta 2-1 a wasan dawowa da aka buga a Madrid.

Lamine Yamal ne ya fara zura ƙwallo wa Barcelona da wuri, bayan ya ci anfani da kuskuren Clement Lenglet, inda ya doke mai tsaron gida Juan Musso.

Daga baya Ferran Torres ya ƙara ta biyu bayan ya karɓi ƙwallo daga Dani Olmo, lamarin da ya sa Barcelona ta matsa lamba.

Sai dai Ademola Lookman ya farke ƙwallo guda ga Atletico, wanda ya dawo da ƙungiyar cikin fafatawar.

Barcelona ta ci gaba da matsa lamba, amma ta gamu da matsala bayan an rage ta zuwa ‘yan wasa 10 sakamakon jan kati da Eric Garcia ya samu.

Duk da ƙoƙarin Robert Lewandowski da Ronald Araujo, Barcelona ta kasa dawowa wasan, inda Atletico ta tabbatar da nasarar tsallakawa zuwa zagayen gaba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker