Duniya
Isra’ila Ta Kashe Kwamandan Hezbollah A Beirut

Wata majiya da ke kusa da Hezbollah ta tabbatar da cewa an kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar a wani hari da Israel ta kai a kudancin birnin Beirut na Lebanon a ranar Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan ne hari na farko da aka kai a yankin cikin kusan wata guda.
Majiyar ta bayyana sunan kwamandan da aka kashe a matsayin Malek Ballout, wanda ake zargin shi ne ke jagorantar ayyukan rundunar Radwan ta kungiyar Hezbollah.
Karanta: Isra’ila Ta Janye Sunan Ministan Iran Daga Jerin Hari
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa shi da kansa ne ya bayar da umarnin kai harin kan kwamandan kungiyar.





