Siyasa

APC Ta Amince Tinubu Ya Tsallake Tantancewar Takarar Zaben 2027

Kwamitin kula da tantance masu neman takara na jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci shiga takarar shugaban kasa ta shekarar 2027 ba tare da an sake gudanar masa da tantancewa ba.

Kwamitin ya ce hakan ya dace da dokoki da ka’idojin cikin gida na jam’iyyar.

An cimma wannan matsaya ne a ranar Laraba bayan zaman da kwamitin ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin kwamitin sun yi nazari kan kundin tsarin mulkin jam’iyyar kafin daukar wannan hukunci.

A cikin wata sanarwa da kakakin APC, Felix Morka ya fitar, ya ce kwamitin ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin jamiyyar ya tanada musamman a sashe na 13.4, sakin layi na (xiii) da (xiv).

Karanta: APC ta tsawaita sayar da fom din takara zuwa Litinin

Ya kara da cewa wadannan tanade-tanade sun bai wa shugaban kasa damar samun tikitin takara kai-tsaye.

Wannan mataki na APC na zuwa ne yayin da harkokin siyasa da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara daukar hankali a fadin Nijeriya, inda jam’iyyu da yan siyasa ke ci gaba da tsara dabarunsu domin tunkarar babban zaben da ke tafe.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker