Duniya

Iran Ta Harbo Jirgi Maras Matuki a Sararin Samaniyar Tehran

Rundunar juyin juya halin Iran ta sanar da cewa ta harbo wani jirgi maras matuƙi samfurin Hermes a sararin samaniyar birnin Tehran.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Mizan sun bayyana cewa rundunar ta yi amfani da sabon tsarin tsaron sararin samaniya wajen kakkaɓo jirgin, wanda ake zargin yana ɗauke da makamai.

Akwai nau’o’in jiragen marasa matuƙi na Hermes da dama da ake amfani da su don ayyuka daban-daban, musamman wajen tattara bayanan sirri da sa ido daga sama.

Sabon samfurin jirgin, mai suna Hermes 900, wanda tsayinsa ya kai kusan mita takwas, na iya yin shawagi a sararin samaniya na tsawon sa’o’i har 36 ba tare da sauka ba.

Iran ta kuma ce tun bayan fara rikicin da ake ciki, ta riga ta lalata jirage marasa matuƙi 132.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker