Labarai

Iran Ta Bude Mashigar Hormuz Ga Jirage

Gwamnatin Iran ta sanar da buɗe Mashigar Hormuz ga dukkan jiragen kasuwanci domin su rika zirga-zirga cikin ’yanci har zuwa ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma.

Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Abbas Araqchi, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya ce an amince da wannan mataki a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya ƙara da cewa za a gudanar da zirga-zirgar ne ta hanyar da aka tsara tun da farko, kamar yadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Iran ta ayyana.

A wani ɓangaren kuma, rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan wani shiri na kawo ƙarshen yaƙin.

Rahoton ya bayyana cewa daga cikin batutuwan da ake dubawa akwai yiwuwar Iran ta miƙa sinadarin uranium, a madadin sakin wasu kuɗaɗen Iran da aka daskarar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker