Duniya

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz kan takaddamar da Amurka

Rundunar sojin Iran ta sanar da sake rufe Mashigar Hormuz, tana mai danganta matakin da ci gaba da takunkumin zirga-zirgar jiragenta da Amurka ke yi.

Rahotanni daga kafofin labaran Iran, ciki har da Fars da IRIB, sun ce rundunar IRGC ta bayyana cewa za a dawo da yanayin mashigar kamar yadda yake a baya, tare da ci gaba da tsaurara tsaro a yankin.

Sojojin Iran sun zargi Amurka da aikata abin da suka kira “fashin teku”, suna mai cewa matakan da ake ɗauka na hana jiragen Iran zirga-zirga sun wuce gona da iri.

Tun da farko Iran ta yi barazanar janye buɗe mashigar ga jiragen ruwa idan har Amurka ba ta janye takunkumin da ta kakabawa jiragenta ba.

Sai dai tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce matakin zai ci gaba har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin gaba ɗaya, yana mai gargadin cewa tsagaita wutar na iya ƙarewa nan ba da jimawa ba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker