Duniya
Gwamnatin Nijar ta rage farashin taki yayin karancinsa a duniya

Gwamnatin Niger ta ɗauki matakin sauƙaƙa farashin taki ga manoma, a daidai lokacin da ake fama da ƙaranci da tsadar sa a sassa daban-daban na duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.
A matakin farko, gwamnatin ta riga ta tura sama da tan dubu 5 na taki zuwa Maradi domin sayarwa ga manoma a farashi mai rahusa.





