Farashin Fetur Ya Tashi zuwa N1,400 a Kano, Jama’a Sun Koka Kan Cikar Lita

Masu amfani da mota da al’ummar Kano sun bayyana damuwarsu kan tashin farashin man fetur tare da zargin wasu gidajen mai da sayar da lita ƙasa da cikakkiyar lita.
Bincike da aka gudanar a yau Litinin ya nuna cewa wasu gidajen mai suna sayar da man fetur tsakanin ₦1,385 zuwa ₦1,400 a kowace lita, abin da ya jawo korafin masu mota da fasinjoji.
Rahotanni sun nuna cewa AA Rano da Aliko Oil suna sayar da litar fetur akan ₦1,385, yayin da a A.A Shafa suna sayar dashi akan ₦1,398 a kowace lita. yayin da Oando PLC ke sayarwa akan ₦1,400 a kowace lita.
Wasu daga cikin masu amfani da man fetur sun ce tashin farashin ya kara tsadar rayuwa, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki. Baya ga farashin, wasu sun kuma koka cewa wasu gidajen mai na sayar da lita ƙasa da cikakken lita, lamarin da ke haifar da zargin rashin gaskiya a ma’aunin sayar da man fetur.
“Mun biya ₦1,400 a lita, amma man da muke samu ba ya cika. Wannan ba adalci ba ne ga masu siya,” in ji wani direba.
Masu Abubuwan hawa sun bukaci hukumomin da suka dace su kara sa ido kan gidajen mai domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen sayar da man fetur.
Al’umma sun kuma yi kira ga Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory (NMDPR) Authority da ta binciki wadannan korafe-korafe tare da tabbatar da cewa gidajen mai suna bin ka’idojin farashi da kuma cikakken ma’aunin lita.
Mutanen gari sun ce tsaurara doka da kuma yin bincike akai-akai a gidajen mai zai taimaka wajen kare masu siya daga zalunci tare da dawo da amincewar jama’a ga tsarin sayar da man fetur.





