FasahaKasuwanci

Cikakken bayani akan InksNation da PinKoin

Bayan sakonni na mutane da suke bukatar karin bayani da kuma haske akan InksNation nayi alkawari zan yi rubutu mai tsawo wanda zai fayyace komai da komai akan InksNation da PinKoin, kafin na fara wani magana zan so su san takaitaccen bayani akaina.

Sunana Yahaya, wanda a ka fi sani da Yahmis, ina harka kwarewa akan computer tun 2009 wanda hakan nasamu horo sosai a kan Cloud Computing da wasu sassa na harkan Computer.

Banda Malami wanda ya koyar da ni aiki da computer a gwanace ( Professionalism ) da iyawa. amma inada magabata wanda a koda yaushe ina alfahari da su.

Na fara transactions na farko a kan Bitcoin ranan 22/10/2016, karfe 22:24 a asusun Bitcoin na Bitx wanda yanzun a ka fi sani da Luno.

Na saya Bitcoin kuma da kudina ranar 25, Oct 2016, karfe 15:19 Bitcoin 0.00635 akan Naira ₦2040 wanda yanzun yakai Naira ₦34,000.

In maganar da nayi bai maka ba ko kuma bai dace da ra’ayin ka ba bana bukatar kace mun komai dalili kuwa ba don dakai nayi rubutu na ba.

Zanyi amfani da wasu kalmomi na Turanci wanda a zahrin gaskia ban san fassarar su da Hausa ba ko kuma na kawo su da turanci dan maganar ya tafi daidai, In kuna karatu kukaga kalmomin da baku fahimce su ba zaku iya copy nasu ku searching a Google domin sanin su tare da cikakken bayani.

Bayani na na farko shine, a kan tambaya kamar haka. Menene InksNation?

InksNation wani hanyane na zunzurutun jan rai da tattaro kudin masu kwadayi wanda iBSmartify suka yi  a cewar su a kan tsari DAO (Decentralized Autonomous Organization) ta hanyar taimakon kai da kai don goge talauci a tsakanin al’umma da alkawarin cewa acikin wata 9 zasu kau da talauci.

iBSmartify Sunce suna kan tsarin BlockChain hakan yasa suka kirkiri InkLedger da PinKoin wanda  Shi InksNation yana amfani da PinKoin a matsayin kudin hada hada da kuma InkLedger a matsayin asusun ajiya.

A ka’idar BlockChain babu wani tsari kamar haka wanda wani zai biya wani ko kuma da zaran mutum yayi rijistar sai abashi wasu makudan kudi wanda bazai iya chanza su ba na bogi sai dai yabi kan Mutane suna bashi ₦1000 yana musu rijistar, ko kuma mutum yasa naira ₦1000 ya samu Naira ₦1,440,000 a shekara.

Abubuwan Lura.

1. wannan ya saba sa hankali da kuma ilimi

2. Babu wani kasuwanci a duniya da zaka sa jarin ₦1000 ka samu ₦100,000 a cikin kwana 30, ko da kuwa sata kakeyi.

3. A duk cikin kudaden Cryptocurrency babu wanda yakai darajan Bitcoin wanda shi kudine wanda duniyar masana ilimin computer suka yarda dashi.

4. Mutane su lura akwai babban ci tsakanin PinKoin da PinkCoin, shi PinKoin an sata sunan PinkCoin ne kamar yanda farkon fitan Bitcoin akayi ta satan sunan bitcoin ana yaudarar mutane ana dan karbe musu chanjin su.

5. In ance BlockChain to dole a sameshi da wannan ka’idojin na farko ya zama

Decentralization babu wani wanda abun ya dogara dashi kafin yayi aiki,

Transparency: komai a fili yake dalla dalla bawai sai kabiya kudin rijistar ko kuma ka saka wani kudi ba, kamar binkwai kawai zan saya Bitcoin ne a wurin wanda yake dashi a farashin da Bitcoin yake a Duniya,

Immutability:  ya zama babu wani gyara da zaa sake masa ko kuma wani chanji, kamar Bitcoin tunda aka kirkiri Bitcoin babu wani Server ko kuma wani abu wai system update ko changes da aka taba yi. Babu wani website kuma a duniya wanda akace wannan mallakar Bitcoin ne ko kuma inda aka kirkiri Bitcoin.

Wannan hujjoji guda biyar ya tabbatar da cewa PinKoin babu abinda ya alakantashi da tsarin Blockchain, kuma babu wani Cryptocurrency mai suna PinKoin a duniyar mu na masu hankali.

Zan dan dakata anan, a rubuna na gaba zan dora akan wani tambayar, da kuma cikakken babban ci tsakanin PinKoin da PinkCoin sai kuma Bitx ( Luno) da kuma InksNation.

Yahaya Shuaibu

Certified Cloud ACA, DNS Admin.

Founder Yahmis NG, Hausa360 & TaskarSo.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker