Babban kuɗin crypto na duniya wato Bitcoin ya samu karin farashi inda ya haura sama da dala 100,000. Idan aka juya wannan farashi zuwa kudin Najeriya wato Naira, ya kai kimanin N160,487,000
Wannan ci gaban ya zama tarihi, domin shi ne karo na farko da Bitcoin ya kai wannan farashi tun bayan kafuwar sa.
Masu saka hannun jari a duniya suna bayyana wannan nasara a matsayin wata babbar dama ga masu zuba jari a duniyar crypto, yayin da masana tattalin arziki ke kallon shi a matsayin wani barazana mai karfi akan kasuwannin duniya.
Wannan karin farashin ya janyo hankalin mutane da dama, musamman ‘yan Najeriya da ke ci gaba da amfani da crypto duk da gwamnatin kasar ta haramta amfani da kuɗin crypto a kasar.