Bahrain Ta Fuskanci Mummunan Harin Makamai a Yau

Kasar Bahrain ta fuskanci wani mummunan hari a yau Talata bayan da rahotanni suka ce makamai masu linzami daga Iran sun fada kan wani sansanin soji a yammacin kasar.
Rahotannin farko sun nuna cewa daya daga cikin makaman ya fada kan sansanin soji na Hamala, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani mai kwantiragin soji ɗan asalin Morocco tare da jikkata mutane da dama.
Mahukuntan Bahrain sun ce mutane da dama sun samu raunuka, ciki har da mutum hudu da ke cikin mawuyacin hali. Yawancin wadanda suka jikkata yan kasar Bahrain ne, ciki har da wasu daga cikin sojoji.
A Bahrain ne kuma United States Navy Fifth Fleet ke da babban sansanin sojin ruwa na United States, duk da cewa rahotanni sun nuna cewa an janye wasu daga cikin dakarun kafin fara rikicin, yayin da wasu jiragen ruwan soji suka bar yankin.
Masana harkokin siyasa sun ce alaƙar Bahrain da Iran ta dade tana cikin tsami, domin Iran na kallon Bahrain a matsayin wani yanki da ta taba mallaka a tarihi. Wannan ya sa dangantakar ƙasashen biyu ta kasance mai rauni idan aka kwatanta da sauran ƙasashen yankin Gulf.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu hare-haren sun faɗa kan tankunan mai, filin jirgin sama, da kuma wasu gidaje a sassa daban-daban na ƙasar.
Bahrain na da yawan al’umma mabiya Shi’a, kuma wasu daga cikinsu na nuna goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sai dai gwamnatin ƙasar ta haramta wa ƴan jarida na ƙasashen waje shiga domin bayar da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa





