Labaran Duniya

Trump Ya Jaddada Ci Gaban Tattaunawa Da Iran

Shugaban kasar Donald Trump ya bayyana cewa tattaunawar da ake gudanarwa tsakanin Amurka da Iran na tafiya cikin tsari da lumana, yana mai cewa ana samun ci gaba mai kyau a tsakanin bangarorin biyu.

Trump ya ce gwamnatinsa ba za ta yi gaggawar cimma yarjejeniya da Iran ba, domin yana son a tabbatar an cimma matsaya mai anfani da dorewa kafin daukar kowane mataki.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu takunkuman da aka kakabawa Iran za su ci gaba da kasancewa har sai an kammala yarjejeniya ta karshe tare da sanya hannu a kanta.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa tattaunawar ta fi kyau idan aka kwatanta da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma a shekarar 2015, wadda ya soki matuka a baya.

Ya ce manufar sabon tsarin ita ce hana Iran mallakar makamin nukiliya tare da samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka hada da sassauta takunkumi, tsaro a yankin Tekun Hormuz da kuma batun shirye shiryen nukiliyar Iran.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker