Labarai
NAHCON ta kammala jigilar mahajjatan Nijeriya 2026 Saudiyya

Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da kammala jigilar maniyyatan Nijeriya na aikin Hajjin shekarar 2026 zuwa kasar Saudiyya.
Hukumar ta bayyana cewa an kammala aikin ne bayan tashin jirgi na karshe da kamfanin jiragen sama Max Air ya yi daga filin jirgin saman Gusau, inda ya dauki maniyyatan jihar Zamfara zuwa kasa mai tsarki.
Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa NAHCON ta ce an gudanar da tashin jirage 98 cikin tsawon kwanaki 18 kacal, inda aka kammala jigilar dukkan mahajjata cikin nasara.
Nijeriya ta kuma samu adadin guraben maniyyata 50,000 domin aikin Hajjin bana.





