Abba Ya Yi Martani Kan Rikicin Siyasar Kano

A yayin wani babban taron siyasa da aka gudanar a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wasu kalamai masu zafi da suka jawo ceceku ce a tsakanin magoya baya da masu bibiyar siyasa.
Mutane da dama na ganin kalaman na nuni ne ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa bai ambaci sunansa kai tsaye ba.
Gwamnan ya bayyana cewa shi mutum ne mai son zaman lafiya da haɗin kai, amma idan aka ci gaba da matsa masa ko muzanta shi, zai fito ya bayyana gaskiya ga jama’a.
Kalaman nasa sun haddasa sabbin muhawara a siyasar Kano, musamman ganin yadda dangantakarsa da tsohon ubangidansa ke kara jawo hankali.
Wannan lamari ya biyo bayan wata hira da aka yi da Sanata Kwankwaso, inda ya bayyana cewa Gwamna Abba zai yi nadamar rabuwa da tafiyar Kwankwasiyya idan har ya ci gaba da daukar wata hanya ta daban.
Wannan furuci ya kara nuna alamun rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu da suka dade suna aiki tare a siyasar jihar Kano.





