Labarai

Kotu Ta Samu Tsohon Ministan Lantarki Da Laifin Badakala

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu tsohon ministan lantarkin Najeriya, Saleh Mamman, da laifuka 12 da suka shafi halasta kuɗaɗen haram da suka kai kimanin naira biliyan 33.

Mai shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, sai dai ya ɗage yanke hukunci na ƙarshe zuwa ranar 13 ga Mayu, 2026, saboda tsohon ministan bai halarci kotun lokacin da aka yanke hukuncin ba.

A wata sanarwa da Economic and Financial Crimes Commission ta wallafa, lauyan hukumar, Rotimi Oyedepo SAN, ya roƙi kotun da ta bayar da sammacin kamo Saleh Mamman domin tabbatar da cewa bai fice daga ƙasar ba kafin ranar yanke hukunci.

Karanta: Umar Ardo Zai Maka NDC Kotu Kan Zargin Saba Ka’idoji

Saleh Mamman ya kasance ministan lantarki daga shekarar 2019 zuwa 2021 a gwamnatin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun kuma nuna cewa a watan Afrilu na wannan shekara, tsohon ministan ya sayi fom ɗin neman takarar gwamnan jihar Taraba ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker